Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki mai take Almarij a yankin Katif, wadda cibiyar kula da shirya gasar karatun kur'ani ta yankin ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, tare da halartar malamai da masana daga yankunan gabacin kasar.
Kamfanin dillancin labarn iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na muzn an habarta cewa, ana shirin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki mai take Almarij a yankin Katif, wadda cibiyar kula da shirya gasar karatun kur'ani ta yankin ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, tare da halartar malamai da masana daga yankunan gabacin kasar ta saudiyya baki daya.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan gasa za a gudanar da ita ne a karo na hudu a yankin, inda daruruwan makaranta da kuma mahardata za su kara juna, daga karshe za afitar da sunayen wadanda suka fi nuna kwazo ta fuskacin harda da kuma kira'a, inda za a basu kyautuka na musamman.
Yanzu haka ana shirin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki mai take Almarij a yankin Katif, wadda cibiyar kula da shirya gasar karatun kur'ani ta yankin ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, tare da halartar malamai da masana daga yankunan gabacin kasar.
770145