IQNA

Haramtacciyar Kasar Yahudawa Na Shirin Kaddamar Da Yaki Kan Gaza

19:48 - April 11, 2011
Lambar Labari: 2104231
Bangaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta fara gudanar da zaman ggagawa kan hare-haren bayan nan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara kaiwa kan alummar yankin zirin Gaza domin tsokanar palastinawa, a shirin da take da shi na sake bude wani sabon yaki kan al'ummar yankin.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kuna na kasar Kuwait an habarta cewa, kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta fara gudanar da zaman ggagawa kan hare-haren bayan nan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara kaiwa kan alummar yankin zirin Gaza domin tsokanar palastinawa, a shirin da take da shi na sake bude wani sabon yaki kan al'ummar yankin na zirin Gaza.

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haramtacciyar kasar ta yahudawan sahyuniya ta fara gudanar da wasu take-take da ke nuni da cewa tana shirin fara kaddamar da wani sabon farmaki kan fararen hular yankin zirin gaza, da nufin dauke hankulan al'ummomin duniya kan ta'asar da take tafkawa.

Kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta fara gudanar da zaman ggagawa kan hare-haren bayan nan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara kaiwa kan alummar yankin zirin Gaza domin tsokanar palastinawa, a shirin da take da shi na sake bude wani sabon yaki kan al'ummar yankin.
771654

captcha