IQNA

Za A Gudanar Da Wani Taro Da Ake Yi Wa take Ranakun Fatimiyya A Karbala

16:23 - April 12, 2011
Lambar Labari: 2104808
Bangaren kasa da kasa, za agudanar da wani zaman taro na addini a birnin Karbala mai alfarma da ke kasar Iraki, wanda ake yi wa taken ranakun Fatimiyya, wanda kuma shi ne karo na hudu za agudanar da wannan babban taro tare da halartar masana da kuma malamai a birnin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun an bayyana cewa, an kammala wani taron wasan kwaikwayo da aka gudanar a birnin Karbala mai alfarma, wanda aka gudanar a kan waki'ar da ta faru da iyalan gidan manzon Allah (SAW) a karkashin jagorancin Imam Hussan (AS) wanda aka kammala a jiya tare da halartar masana.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro ya samu karbuwa daga masana daga sassa daban-daban na kasar Iraki, kamar dubban masu ziyarar hubbaren Imam Hussain mai tsarki suka halarci wannan zaman taro a wasan kwaikwayo, wanda ke nuni da takamai abin da ya faru da zuriyar manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa.

An kammala wani taron wasan kwaikwayo da aka gudanar a birnin Karbala mai alfarma, wanda aka gudanar a kan waki'ar da ta faru da iyalan gidan manzon Allah (SAW) a karkashin jagorancin Imam Hussan (AS) wanda aka kammala a jiya a birnin mai alfarma.
772274
captcha