IQNA

An Buga Tare Da Yada Littafin Sanin Hanyoyin Hardar Kur'ani Mai Tsarki

12:09 - April 13, 2011
Lambar Labari: 2105211
Bangaren kasa da kasa, an buga tare da yada wani littafi mai suna sanin hanyoyin hardar kur'ani mai tsarki a saukake, wanda cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta sayyida Rukkaya (SA) da ke birnin kum ta dauki nauyin wallafa shi, wanda kuma shi ne irinsa na shida da ta wallafa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na birnin Kum an habarta cewa, an buga tare da yada wani littafi mai suna sanin hanyoyin hardar kur'ani mai tsarki a saukake, wanda cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta sayyida Rukkaya (SA) da ke birnin kum ta dauki nauyin wallafa shi, wanda kuma shi ne irinsa na shida da ta wallafa duk akan hanyoyin koyon harda.

An yi amfani da hanyoyi masu sauki ta yadda dalibai masu koyon hardar kur'ani mai tsarki za su iya binsu ba tare da wata wahala ba, kuma an kasa bangarorin kur'ani zuwa wasu adadin kwanaki da watanni ko shekaru, daidai da yadda mai karau yake son ya yi amfani da shi domin koyon hardar a cikin hanyar da yake bukata, mai sauri ko kuma bin hanya mai sauki.

Buga tare da yada wani littafi mai suna sanin hanyoyin hardar kur'ani mai tsarki a saukake, wanda cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta sayyida Rukkaya (SA) da ke birnin kum ta dauki nauyin wallafa shi, wanda kuma shi ne irinsa na shida da ta wallafa, zai taimak matuka ga masu bukatar shiga tafarkin harda.

773185


captcha