IQNA

Gudanar Da Taron Kara Wa Juna Sani Kan Manzon Allah (SAW) A Kasar Turkiya

17:41 - April 16, 2011
Lambar Labari: 2106582
Bangaren siyasa da zamantakewa, an gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani dangane da sakon addinin musulunci wanda aka yi wa take da manzon Allah rahma ga al’ummar duniya, wanda aka gudanar a kasar Turkiya tare da halartar pira ministan kasar Rajab Tayyib Ardugan a birnin Istanbul fadar mulkin kasar domin girmama manzon Allah.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani dangane da sakon addinin musulunci wanda aka yi wa take da manzon Allah rahma ga al’ummar duniya, wanda aka gudanar a kasar Turkiya tare da halartar pira ministan kasar Rajab Tayyib Ardugan a birnin Istanbul fadar mulkin kasar domin girmama manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa.
Shi dai wannan zaman taro dai an shirya shi da nufin kara babbana matsayin addinin musulunci da manzon Allah (SAW) ya zo da shi daga Allah madaukakin sarki, dangane da lamurra da dama da suka danganci rayuwar dan adam ta yau da kullum, wanda kuma taro ne da ke samun halartar wakilai daga kungiyoin musulmi daban-daban na kasar Turkiya, da kuma manyan jami’an gwamnati.
Ana ganin cewa gudanar da wannan zaman taro na karawa juna sani dangane da sakon addinin musulunci wanda aka yi wa take da manzon Allah rahma ga al’ummar duniya, wanda aka gudanar a kasar Turkiya tare da halartar pira ministan kasar Rajab Tayyib Ardugan a birnin Istanbul fadar mulkin kasar domin girmama manzon Allah, manuniya ce kan abban cigaban da aka samu ta wayewa kan addinin muslunci a kasar Turkiya.
774472


captcha