IQNA

Malaman Addini kasar Bahrain Sun Bukaci A Gudanar Da Sauye-Sauye Na Siyasa

21:16 - April 17, 2011
Lambar Labari: 2107280
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya dangane da matsayin al'ummar kasar na neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a cikin harkokin mulki da siyasar kasar, maimakon mayar da gidan sarauta shi ne wuka a shi ne nama a cikin dukkanin harkokin kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya dangane da matsayin al'ummar kasar na neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a cikin harkokin mulki da siyasar kasar, maimakon mayar da gidan sarauta shi ne wuka a shi ne nama a cikin dukkanin harkokin kasar ta Bahrain.

Malamin ya ci gaba da cewa abin mahukuntan kasar ta Barain suka yi ya tabbatar da cewa ba manufarsu ce gudanar da sauye-sauyen siyasar da suka furta bat un farko, inda suke yin amfani da karfin soji domin murkushe dukkanin masu neman a yi garanbawul, wanda hakan ya yi hannun riga da dukkanin hakkoki na al'ummar kasar.

Babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya dangane da matsayin al'ummar kasar na neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a cikin harkokin mulki da siyasar kasar, maimakon mayar da gidan sarauta shi ne wuka a shi ne nama a cikin dukkanin harkokin kasar.

775072



captcha