IQNA

An Kafa Cibiyar Muslunci Ta Jahar Minesuta A Kasar Amurka

21:16 - April 17, 2011
Lambar Labari: 2107284
Bangaren kasa da kasa, musulmi mazauna jahar Minesuta ta kasar Amurka sun bayyana cewa sun kafa wata babbar cibiyar addinin muslunci a jahar, wadda za ta kula da ayyukan musulmin jahar na addinisu da kuma harkokinsu na yau da kullum daidai da koyarwar addininsu.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na MPRN news an bayyana cewa, musulmi mazauna jahar Minesuta ta kasar Amurka sun bayyana cewa sun kafa wata babbar cibiyar addinin muslunci a jahar, wadda za ta kula da ayyukan musulmin jahar na addinisu da kuma harkokinsu na yau da kullum daidai da koyarwar addininsu da kuma harkokin zamantakewa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wanann zaman taro yan ada matukar muhimamnci bisa la'akari da cewa da dama daga cikin musulmin kasar amurka suna da bukatar wayar da kai da kuma tunatarwa kan abubuwan da ya kamata su mayar da hanakali kansu dangane da addini, da kuma wasu lamurran da suka danganci rayuwarsu ta zamantakewa.

An gudanar da bababn taron musulmin kasar Amurka na jahar Penselvania, inda suke gudanar tatatunawa kan muhimman ayyukan da suka danganci harkokin addinin Musulunci da kuma yadda za su kara fadada lamurransu ba tare da samun wata tsangwama daga sauran bangarori ba.

774751

captcha