Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da tarukan zabar birnin Tilmisan kasar Algeria a matsayin babban birnin al’adun musulunci na shekara ta 2011, wanda babbar kungiyar kasashen musulmi ta OIC take zaba akowace shekara, tare da amincewar dukkanin mambobi na kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO an bayyana cewa, an fara gudanar da tarukan zabar birnin Tilmisan kasar Algeria a matsayin babban birnin al’adun musulunci na shekara ta 2011, wanda babbar kungiyar kasashen musulmi ta OIC take zaba akowace shekara, tare da amincewar dukkanin mambobi na kasashen musulmi, wanda bangaren kula da harkokin al’adu da ilimi na kungiyar ke gudanarwa.
A bangare guda kuma a cikin wani byani da ya fitar bababn sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi, ya bayyana irin wadannan ayyuka na ta'addanci da gwamnatin yahudawan sahyuniyan take aikatawa kan fararen hula palastinawa da cewa aiki ne da ya yi hannaun riga da dukaknin ka'idoji da kuma dokoki na kasa da kasa, a akn ya kirayi dukkanin gwamnatoci masu fada a ji da suke safke nauyin da ya rataya kansu.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, an fara gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Nuakshaut fadar mulkin kasar Mauritaniya tare da halartar masana da kuma makaranta gami da mahardata na kasar ta Mauritania. 775501