IQNA

Mabiya Addinai Dole Su Yi Kokari Wajen Samun Fahimtar Juna Ta Bai Daya

14:35 - April 20, 2011
Lambar Labari: 2109192
Bangaren kasa da kasa, mahalarta taron tattaunawar addinai ta bai daya tsakanin addinan musulunci da kuma Buda, sun hadu kan cewa dole ne dukkanin mabiya addinai a duniya su taka gaggarumar rawa wajen samar da fahimtar juna tsakanin dukkanin al’ummomi, tare da zaman lafiya da girmama ra’ayoyi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin yanar guizo na banagaren yada labaransa daga birnin Qom an bayyana cewa, mahalarta taron tattaunawar addinai ta bai daya tsakanin addinan musulunci da kuma Buda, sun hadu kan cewa dole ne dukkanin mabiya addinai a duniya su taka gaggarumar rawa wajen samar da fahimtar juna tsakanin dukkanin al’ummomi, tare da zaman lafiya da girmama ra’ayoyi dukkanin bangarori.
Wadannan addinai biyu muslunci da kuma addinin Buda, dukkaninsu addinai da suke da manufa fahimtar juna tsakaninsu da sauran addinai, duk da irin banbancin akida ta addini da ke akwai tsakaninsu, amma sun hadu a kan wasu abubuwa na ‘yan adamtaka, wadanda suke da matukar muhimamnci a rayuwar dan adam ga abki daya.
An gudanar da wannan zaman tattaunawa tsakanin addinai biyu na muslunci da kuma Buda, wanda shi ne karo na biyu a birnin qom da ke jamhuriyar muslunci ta Iran, tare da halartar masana daga dukkanin bangarorin mabiya addinan guda biyu, kuma masana sun bayar da gudunmawarsu a taron da aka gunar a karo na biyu.
776731
captcha