Bangaren kasa da kasa,. an gudanar da wani zaman taro na yin nazari kan sirar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a birnin Dubai babbar cibiyar kasuwanci da attalin arziki ta kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halaratar masana da kuma malamai daga kasashen duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar albayan ta kasar UAE an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro na yin nazari kan sirar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a birnin Dubai babbar cibiyar kasuwanci da attalin arziki ta kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halaratar masana da kuma malamai daga kasashen larabawa musamman.
A yayin gudanar da wannan zaman taron an yi bahasi kan sirar ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa, wanda hakan zai kara bayar da damar sanin wannan manzo mai madaukakakin matsayi, kuma taron ya zo ne adaidai lokacin da wasu daga cikin al’ummomin kasashen turai suke da kokarin dushe hasken sakon da ya zo da shi ga dan adam daga Allah madaukakin sarki.
an gudanar da wani zaman taro na yin nazari kan sirar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a birnin Dubai babbar cibiyar kasuwanci da attalin arziki ta kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halaratar masana da kuma malamai daga kasashen daban-daban. 777675