IQNA

Bincike Kan Rawar da Hukumar Kula Da Ilimi Ta Asesko Ke takawa

18:01 - April 21, 2011
Lambar Labari: 2109643
Bangaren kasa da kasa: daga daya ga watan Urdebesht na shekarar hijira shamsiya ta dubu daya da dari uku da tis'in a birnin Dubai birnin kasuwanci na hadeddiyar daular larabawa za a gudanar da wani taro day a shafi bincike irin rawar da hukumar Asesko mai kula da ilimi da al'adu a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ke takawa ta fuskar ilimi.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ikna ne ya watsa rahoton cewa; daga daya ga watan Urdebesht na shekarar hijira shamsiya ta dubu daya da dari uku da tis'in a birnin Dubai birnin kasuwanci na hadeddiyar daular larabawa za a gudanar da wani taro day a shafi bincike irin rawar da hukumar Asesko mai kula da ilimi da al'adu a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ke takawa ta fuskar ilimi. A wajan wannan taro za a hada masana da malamai da suka fito daga kasashe da dabn-daban na musulmi mambobin wannan kungiyar ta hadin kan kasashen musulmi da za su yi nazari da masanyar tunani da nazari kan irin rawar da wannan hukuma ke takawa da kuma hanyoyin da za a bi domin ganin an kara karfi da aikin da hukumar ke gudanarwa.


777508

captcha