IQNA

An Jaddada Muhimamncin Hada Kai Tsakanin Malaman Musulmi Na Duniya

15:09 - April 24, 2011
Lambar Labari: 2111105
Bangaren kasa da kasa, shugaban cibiyar jami’at Islami na kasar pakistan ya kirayi dukkanin malaman addinin muslunci da kuma masana, da su ajiye duk banbancin fahimta a gefe, su hada kai domin tunkarar makircin da ake kulla wa addinin muslunci, inda ya ce wanmnan wajibi ne da ya rataya kansu baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar the News an bayyana cewa, shugaban cibiyar jami’at Islami na kasar pakistan ya kirayi dukkanin malaman addinin muslunci da kuma masana, da su ajiye duk banbancin fahimta a gefe, su hada kai domin tunkarar makircin da ake kulla wa addinin muslunci, inda ya ce wanmnan wajibi ne da ya rataya kansu baki daya ba tare da fitar da wani bangare ba.
A banagare guda kuma an gudanar dawani zaman taro a kasar Birtaniya na mabiya addnin muslunci, a yayin gudanar da zama masana da malaman jami’oi za su halarta kuma za su gabatar da laccoci ga mahalrta taron, daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hankali kansu akwai nazari kan matsayin sharia a cikin addinin muslunci, da kuma yadda wannan addini mai tsarki yake kallon rayuwar zamantakewa ta jama’a.
Rahoton ya tabbatar da cewa a cikin wata mai kamawa ne za a gudanar da wani zama na karawa juna sani kan nazarin addinin musulunci, wanda za a gudanar a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar Lise da ke kasar Birtaniya a karon farko.
779089
captcha