IQNA

Musulmin Kasar Faransa Sun Yi Allawadai Da Keta Alfarmar Wani Masallaci A Kasar

16:09 - April 26, 2011
Lambar Labari: 2112570
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci na kasar faransa sun yi kakkausar suka kan keta alfarmar wani masallaci da aka yi a garin Renes na kasar, inda suka bayyana hakan a matsayin wani mataki na tsokanar mabiya addinin muslunci na duniya baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo CFCM an bayyana cewa, mabiya addinin muslunci na kasar faransa sun yi kakkausar suka kan keta alfarmar wani masallaci da aka yi a garin Renes na kasar, inda suka bayyana hakan a matsayin wani mataki na tsokanar mabiya addinin muslunci na duniya ba na kasar Faransa ba kawai.
A rahoton kuma an bayyana cewa wasu yankunan kasar faransa suna da musulmi da dama, wasu kuma akwai karancin musulmia acikinsu, saboda haka ya kamata har wadanda suke da karancin musulmin a basu damar shiga cikin wannan zabe, ta yadda hakkin wani ba zai saraya ba, wanda kuma hakan na bukatr karin lokaci kafin hada sunayen dukkanin musulmin yankuna.
Shugaban masallacin birnin paris fadar mulkin kasar Faransa Dalil Bubakar ya bukaci da a dage gudanar da zaben shugaban kwamitin musulmin kasar Faransa zuwa wani lokaci nan gaba ne, saboda rashin samun daidaito tsakanin musulmin yankunan kasar, da kuma yin adalci a wurin zaben kmar yadda ya kamata.
780319


captcha