IQNA

Babban Malamin Addini A Kasar Lebanon Ya Yi Kiran Taro Kan Batun Bahrain

19:31 - April 27, 2011
Lambar Labari: 2113405
Bangaren kasa da kasa, bababn malamin addinin muslunci kuma mataimakin shugaban majalisar mabiya addinin muslunci daga mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar, ya yi kira da a gudanar da wani zaman taro kan domin tattauna abin da ke faruwa kan al'ummar kasar Bahrain daga azzaluman mahukuntan kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar al-intiqad cewa, bababn malamin addinin muslunci kuma mataimakin shugaban majalisar mabiya addinin muslunci daga mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar, ya yi kira da a gudanar da wani zaman taro kan domin tattauna abin da ke faruwa kan al'ummar kasar Bahrain daga azzaluman mahukuntan kasar, tare da hada baki da mahukuntan kasar Saudiyya.

Ayatollah Abdulamir Kabalan ya bayyana cewa al'ummar kasar Bahrain da suke fuskantar zauncin duniya, suna da matukar bukatuwa zuwa ga taimakon dukkanin musulmi masu 'yancin siyasa da kuma kin zalunci a kan raunana, a kan haka ya rataya kan kungiyoyin kare hakkin bil adama su taka gagarumar rawa wajen bayyana wa duniya halin kunci da al'ummar Bahrain suke ciki.

Bababn malamin addinin muslunci kuma mataimakin shugaban majalisar mabiya addinin muslunci daga mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar, ya yi kira da a gudanar da wani zaman taro kan domin tattauna abin da ke faruwa kan al'ummar kasar Bahrain daga azzaluman mahukuntan kasar.

781310





captcha