Bangaren kasa da kasa, ma’atar kula da ayyukan leken asiri a haramtacciyar kasar Isra’ila ta bukaci da a daina watsa kiran salla a cikin masallatan birnin Qods, amma babban gamayyar kungiyoyi da cibiyoyin muslunci ta birnin Qods ta ki amincewa da hakan, tare da bayyana cewa wannan wani yunkuri na wuce gona da iri.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin yanar gizo na islamtoday cewa, ma’atar kula da ayyukan leken asiri a haramtacciyar kasar Isra’ila ta bukaci da a daina watsa kiran salla a cikin masallatan birnin Qods, amma babban gamayyar kungiyoyi da cibiyoyin muslunci ta birnin Qods ta ki amincewa da hakan, tare da bayyana cewa wannan wani yunkuri na wuce gona da iri daga bangaren haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba.
Gudanar da sallar juma’a abirnin Rom fadar mulkin kasar Italia a babban dandalin da ke tsakiyar birnin, domin nuna rashin amincewa da matakin da mahukuntan suka dauka na kin bayar da izinin gina masallaci a birnin, na tattare da babban sako.
782306