IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Karatun Kur’ani Ta Dalibai Jami’a A Burnei

15:26 - April 28, 2011
Lambar Labari: 2113618
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta matasa a kasar Burnei, wadda ta kebanci daliban makarantun firamare da sakandare a yankin Blait, inda yanzu haka suke ci gaba da karawa a juna bangarori daban-daban na tilawa da kuma karatun tajwidi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bru Direct an bayyana cewa, an fara gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta matasa a kasar Burnei, wadda ta kebanci daliban makarantun firamare da sakandare a yankin Blait, inda yanzu haka suke ci gaba da karawa a juna bangarori daban-daban na tilawa da kuma karatun tajwidi da dukkanin sauran bangarorin da ake gudanar da harda a kansu.
A wani labari kuma da ya nakalto daga shafin yanar gizo na le-coran an bayyana cewa, an saka tarjamar kur’ani mai tsarki a cikin shafin yanar gizo a cikin harshen farasanci, tare da karatun kur’ani mai tsarki daga fitattun makaranta na duniyar musulmi, da nufin kara fadada ayyukan kur’ani a shafukan yanar gizo da ake ziyarta koina cikin duniya.
Bugu da kari kan tarjamar kur’ani mai tsarki a acikin harshen faranci dake cikin wannan shafi na yanar gizo, za a iya sanin wasu abubuwan da suka shafi kur’ani, kamar sanin adadin ayoyin da ke cikin sura, ko kuma dalilan safkar ayoyi da kuma tafsirin ma’nar wasu kalmomin kur’ani, da suke bukar bayani ta yadda mai karatu ba zai sha wahala wajen gane ma’narsu ba.
782282

captcha