IQNA

Misrawa Na Bukatar A Fitar Da Dokokin Kasarsu Daga Kur’ani Mai Tsarki

15:24 - April 28, 2011
Lambar Labari: 2113621
Bangaren kasa da kasa, sakamakon wani jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar Masar ya yi nuni da cewa akasarin al’ummar kasar na bukatar ganin an fitar da dokokin da ke cikin kundin tsarin mulki daga kur’ani mai tsarki, maimakon irin tsarin da ya gabata wanda babu ruwansa da addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na associated Press an bayyana cewa, sakamakon wani jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar Masar ya yi nuni da cewa akasarin al’ummar kasar na bukatar ganin an fitar da dokokin da ke cikin kundin tsarin mulki daga kur’ani mai tsarki, maimakon irin tsarin da ya gabata wanda babu ruwansa da addinin muslunci a dukkanin lamurransa.
Da dama daga cikin wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun bayyana cewa su dai musulmi ne, kuma wajibi ne dokokin kasarsu su yi daidai da koyarwar addininsu, ba tare da kuma an takura wani bangare ba, ta yadda za aiya baiwa kowa hakkinsa kamar yadda ya kamata amatsayinsa na dan kansa, kuma sun yi imanin cewa dokokinsu za su dace da musulunci kasantuwarsu musulmi.
Sakamakon jin ra’ayin jama’ar da aka gudanar a kasar Masar ya yi nuni da cewa akasarin al’ummar kasar na bukatar ganin an fitar da dokokin da ke cikin kundin tsarin mulki daga kur’ani mai tsarki, maimakon irin tsarin da ya gabata wanda babu ruwansa da addinin muslunci, maimakon haka ma ya shiga gaba da addinin ne.
782226
captcha