IQNA

Musulmin Kasar Swizerland Da Suka Musulunta Za Su Gudanar Da Taro

12:53 - May 05, 2011
Lambar Labari: 2117749
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Switzerland da suka musulunta za su gudanar da wani zama domin yin bitar irin ci gaban da suka samu bayan karbar addinin muslunci a matsayin addininsu, wanda kuma za su ci gaba da yin hakan a shekara-shekara.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-islam an bayyana cewa, musulmin kasar Switzerland da suka musulunta za su gudanar da wani zama domin yin bitar irin ci gaban da suka samu bayan karbar addinin muslunci a matsayin addininsu, wanda kuma za su ci gaba da yin hakan a shekara-shekara domin samun karfafa gwiwar junansu.

Kasar Switzerland dai na daga cikin kasashen da suka bi sahun siyasar wasu kasashen turai ta nuna kyam aga addinin muslunci, inda suka gabatar da wani daftarin doka da ke neman a hana gina masallatai a kasar, kuma mambobin majalisa suka amince da hakan.

Mabiya addinin muslunci na kasar Switzerland da suka musulunta za su gudanar da wani zama domin yin bitar irin ci gaban da suka samu bayan karbar addinin muslunci a matsayin addininsu, wanda kuma za su ci gaba da yin hakan a shekara-shekara, wanda zai fara daga wannan da muke ciki.

786469



captcha