Bangaren kasa da kasa;a ranar sha shidda ga watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijara shamsiya bayan sallar juma'a a kasar Saudiya matasan kasar karkashin kiran da hadin guiwar kungiyoyin matasa na kasar ta Saudiya suka yi sun amsa wannan kira ta hanyar gudanar da zangfa-zanga.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Irna ne ya watsa rahoton cewa; a ranar sha shidda ga watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijara shamsiya bayan sallar juma'a a kasar Saudiya matasan kasar karkashin kiran da hadin guiwar kungiyoyin matasa na kasar ta Saudiya suka yi sun amsa wannan kira ta hanyar gudanar da zangfa-zanga. A daidai lokacin da sojojin kasar Saudiya ke ci gaba da yin kisan gilla da kisan kiyashi kan al'ummar Bahrain da ke son kawo canji da sauye-sauye a kasarsu ,matasan kasar Saudiya sun gudanar da zanga-zanga da a cikin suke goyan bayan al'ummar Bahrain da ake gallazawa .
787361