Bangaren kasa da kasa, gidan sarautar ali-khalifa na kasar Bahrain shi ne abin da ke tabbatar da ta’addancin gwamnati, bayan kone masallatai da rusa gidajen mutane da suke yi da cin zarafin dan adam na zahiri da badini a dukkanin fadin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, daya daga cikin fitattun ‘yan siyasar kasar Bahrain Kasim Hashimi ya bayyana cewa, gidan sarautar ali-khalifa na kasar Bahrain shi ne abin da ke tabbatar da ta’addancin gwamnati, bayan kone masallatai da rusa gidajen mutane da suke yi da cin zarafin dan adam na zahiri da badini a dukkanin fadin kasar ta Bahrain.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muzn an bayyana cewa, an dage gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar Bahrain mai taken zikrull hakim da ake gudanarwa duk shekara a kasar, sakamakon abubuwan da suke faruwa a halin yanzu na cin zarafin al’ummar muslmi da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da suka yi, tare da hadin gwiwa da gwamnatin wahabiyawan saudiyya.
Daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Bahrain Abdulkarin Abduljalil ya bayyana cewa, mutanen kasar Bahrain sun mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu bore a fadin kasar. 792269