Bangaren kasa da kasa, ana samun babban ci gaba ta fuskacin koyar da ilmomin addinin muslunci a kasar Malazia, duk kuwa da matsalar da ake fama da ita ta karancin malamai, kasantuwar kasar daya daga cikin kasashen musulmi da suka samu gagarumin ci gaba ta fuskoki da dama.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Conferencealert an bayyana cewa, ana samun babban ci gaba ta fuskacin koyar da ilmomin addinin muslunci a kasar Malazia, duk kuwa da matsalar da ake fama da ita ta karancin malamai, kasantuwar kasar daya daga cikin kasashen musulmi da suka samu gagarumin ci gaba ta fuskoki da dama a wannan zamani.
Bayanin ya ci gaba da cewa, Wasu bayanan sun tabbatar da cewa, tun bayan da ma'aikatar kula da ayyukan addinin ta kasar saudiyya ta bayyana hakan, da dama daga cikin masana da manazarta sun bayyana cewa hakan zai taimaka musu matuka, matukar dai za a samar da littafai na sahihin tarihi wanda ba agurbata ba, ko saka ra'ayi na bangaranci da nufin tallata wata akida.
Ali-sheikh babban daraktan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ya bayyana cewa za abude wata bababr cibiyar kula da bincike da nazari kan tarihin manzon Allah (SAW) a birnin Jidda na kasar, domin bayar da dama ga masu bincike su kara fadada ayyukansu ta wannan fuska.
794244