IQNA

Yarjejeniyar Janye Sojojin Mamayar Amurka Daga Iraki Ba Za Ta Sabuntu Ba

13:47 - May 29, 2011
Lambar Labari: 2130207
Bangaren kasa da kasa, babban limammin masallacin birnin Najaf na kasar Iraki ya bayyana cewa, yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin bangaren gwamnatin Iraki da kuma Amurkawa kan janye dakarunsu daga kasar zuwa karshen shekarar nan ba za ta taba canjawa ba.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, Sayyid Sadruddin babban limammin masallacin birnin Najaf na kasar Iraki ya bayyana cewa, yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin bangaren gwamnatin Iraki da kuma Amurkawa kan janye dakarunsu daga kasar zuwa karshen shekarar nan ba za ta taba canjawa ba kamar yadda wasu suke neman tayar da wannan yarjejeniya.

Kakakin kungiyar tarayyar turai Jerzy Buzek, ya fadi jiya cewa ko alama ba za su amince da hukuncin kisan da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan matasan hudu ba, kuma kungiyar tana yin kira ga mahukuntan kasar ta Bahrain ta kawo karshen yin amfani da karfin da take yi kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauyen siyasa a kasar.
A jiya ne wata kotun soji da mahukuntan Bahrain suka kafa cikin makwannin suka, ta yanke hukuncin kisa kan wasu matasa hudu, bisa zargin cewa suna da hannu wajen mutuwar 'yan sanda biyu a lokacin gudanar da zanga-zanga a birnin Manama.
Al'ummomin duniya da dama da suka hada da kungiyoyin kare hakkin bil adama, suna ci gaba da yin Alawadai da mahukuntan kasar Bahrain da kuma na Saudiyya, sakamakon yin amfani da karfin soji da suka yi wajen yin kisan gilla a kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa ta hanyar lumamana a cikin kasar ta Bahrain.
799407

captcha