Bangaren kasa da kasa, babban limamin masallacin birrnin Sofia na kasar Bugaria ya bukaci mahukuntan kasar da su bayar da damar gina wani babban masallaci a birnin, duk kuwa da irin adawar da masu kiyayya da muslunci na kasar suke nunawa kan hakan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IINA an bayyana cewa, babban limamin masallacin birrnin Sofia na kasar Bugaria ya bukaci mahukuntan kasar da su bayar da damar gina wani babban masallaci a birnin, duk kuwa da irin adawar da masu kiyayya da muslunci na kasar suke nunawa kan hakan musamman ma a cikin lokutan nan.
A wani labarin kuma da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo CFCM an bayyana cewa, mabiya addinin muslunci na kasar faransa sun yi kakkausar suka kan keta alfarmar wani masallaci da aka yi a garin Renes na kasar, inda suka bayyana hakan a matsayin wani mataki na tsokanar mabiya addinin muslunci na duniya ba na kasar Faransa ba kawai.
A rahoton kuma an bayyana cewa wasu yankunan kasar faransa suna da musulmi da dama, wasu kuma akwai karancin musulmia acikinsu, saboda haka ya kamata har wadanda suke da karancin musulmin a basu damar shiga cikin wannan zabe, ta yadda hakkin wani ba zai saraya ba, wanda kuma hakan na bukatr karin lokaci kafin hada sunayen dukkanin musulmin yankuna.
800148