IQNA

Imam Khomeini (RA) Ya Fadakar Da Al’umma Kan Manufar Yammaci Da Gabbaci

17:01 - June 05, 2011
Lambar Labari: 2133235
Bnagaren kasa da kasa, marigayi Imam Khomeini ya baiwa mata dukkanin hakkokinsu tare da kare mutuncinsu bisa dogaro da koyarwar kur'ani mai tsarkan hakan, wanda hakan ne babban sirrin da ya sanya mata suka samu matsayinsu da 'yancinsu da addinin Musulunci ya ba su a kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo an bayyana cewa, Mostafa Golam Hossein ya bayyana cewa marigayi Imam Khomeini ya baiwa mata dukkanin hakkokinsu tare da kare mutuncinsu bisa dogaro da koyarwar kur'ani mai tsarkan hakan, wanda hakan ne babban sirrin da ya sanya mata suka samu matsayinsu da 'yancinsu da addinin Musulunci ya ba su a jamhuriyar muslunci bayan samun nasarar juyin.
Ya ci gaba da cewa mata sun kasance a kasar Iran kafin samun nasarar juyin juya halin muslunci abin tausayi matuka, kasantuwarsu ba su da matsayi irin na dan adam, kuma ana yin mu'amala da su tamkar ba mutane ba, amma bayan yunkurin Imam ya yi nasara sun samu 'yanci bisa mahangar muslunci, wanda hakan ya mayar da su mutane.
Wani masana da kasar Kuwait ya bayyana cewa, marigayi Imam Khomeini ya baiwa mata dukkanin hakkokinsu tare da kare mutuncinsu bisa dogaro da koyarwar kur'ani mai tsarkan hakan, wanda hakan ne babban sirrin da ya sanya mata suka samu matsayinsu da 'yancinsu da addinin Musulunci ya ba su a kasar.
803257




captcha