Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zama na malaman makarantun kur'ani mai tsarki a garin Nasiriyya na kasar Iraki, inda aka gabatar da bayanai da suka danganci irin muhimmancin da ke tattare da makarantun kur'ani da kuma rawar da suke takawa wajen shiryar da jama'a zuwa ga sahihin tafarkin addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an gudanar da wani zama na malaman makarantun kur'ani mai tsarki a garin Nasiriyya na kasar Iraki, inda aka gabatar da bayanai da suka danganci irin muhimmancin da ke tattare da makarantun kur'ani da kuma rawar da suke takawa wajen shiryar da jama'a zuwa ga sahihin tafarkin addini kamar yadda kur'ani ya nuna.
A wani labari da ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo na leprogre an bayyana cewa, 'yan sandan kasar faransa sun kame wasu masu keta alfamar masattai a kasar, bayan da mabiya addinin muslunci na kasar suka koka kan yadda wasu masu tsananin gaba da addinin muslunci suke daukar wasu sabbin matakai na tsokana a cikin lokutan nan domin fusata musulmi.
Rahoton ya ci gaba da cewa kasar faransa wadda ita ce kasar da ke da yawon adadin muslumi da suke a matsayi na biyu wajen yawa bayan addinin kirista a kasar, inda ake sa ran adadin nasu yake ci gaba da karuwa tare da lunlunkawa a cikin shekaru masu zuwa a nan gaba.
811234