Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta birnin Jidda na kasar Saudiyya ta shirya gudanar da wani bayar da horo ga yara 'yan makaranta da suka samu hutu a makarntunsu a bazarar wannan shekara, inda za akoyar da su karatu da hardar kur'ani mai tasrki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta birnin Jidda na kasar Saudiyya ta shirya gudanar da wani bayar da horo ga yara 'yan makaranta da suka samu hutu a makarntunsu a bazarar wannan shekara, inda za akoyar da su karatu da hardar kur'ani mai tasrki kamar dai yadda ta saba gudanarwa akowace shekara.
Wani rahoto da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut an bayyana cewa, wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Lebanon Malam Muhammadi a lokacin da yake kai wata ziyara wa jagoran kirista na kasar Lebanon Bushara Al-rai ya bayyana cewa, mabiya addinin kirista na kasar Iran suna samun hakkokinsu kamar sauran musulmin kasar ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu ba, duk kuwa da cewa adadinsu kadan ne matuka a kasar ta Iran.
A bangare guda bayanin ya ci gaba da cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Auzbakistan ta gudanar da zama, domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci mabiya addinin muslunci na kasar, musamman ma matsalolin da suke fuskanta ta fuskacin karancin ilimi da sauransu. 811710