IQNA

Al'ummar Kasar Bahrain Na Ci Gaba Da Gudanar Da Zangar-Zangar Neman Sauyi

13:54 - June 23, 2011
Lambar Labari: 2143127
Bangaren kasa da kasa, mutanen garuruwa daban-daban akasar Bahrain na ci gab ada gudanar da zanga-zangar neman sauyi, tare da nuna rashin amincewarsu da mulkin zalunci da danniya na sarakunan kasar da suke yin amfani da karfin bindiga wajen yin kisan kiyashi a kan fararen hula.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na aljazeera an bayyana cewa, mutanen garuruwa daban-daban akasar Bahrain na ci gab ada gudanar da zanga-zangar neman sauyi, tare da nuna rashin amincewarsu da mulkin zalunci da danniya na sarakunan kasar da suke yin amfani da karfin bindiga wajen yin kisan kiyashi a kan fararen hula da suke neman sauyi na siyasa a kasar.

Zanga-zangar da aka gudanar da jiya a dukkanin fadin kasar Bahrain, ta yi Allawadai da mahukuntan kasar baki daya, kan yanke hukunci na zalunci da suke yi kan masu neman sauyi, da kuma jagororin jam'iyun adawa, gami da na kungiyoyin kare hakkin bil adama, daga cikin kuwa har da yanke hukuncin daurin rai da rai da mahukuntan Bahrain din suka yi jiya a kan wasu jagororin 'yan adawa.

Mutanen garuruwa daban-daban akasar Bahrain na ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman sauyi, tare da nuna rashin amincewarsu da mulkin zalunci da danniya na sarakunan kasar da suke yin amfani da karfin bindiga wajen yin kisan kiyashi a kan fararen hula.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam daga kasashen duniya suna ci gaba da yin Allawadai da wannan mataki na zalunci da kama karya da mahukuntan kasar ta Bahrain suke dauka, duk kuwa da cewa suna yin hakan ne tare da cikakken goyon bayan Amurka da sauran kasashen yammacin turai.

813451
captcha