Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na IFESI an bayyana cewa, an sanar da sabon tsarin harkokin tattalin arzikin musulmin kasar Faransa, da nufin kara bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki na musulmin kasar ta dukkanin bangarori na tattalin arziki.
Wani rahoton kuma ya ce pira ministan gwamnatin rikon kwarya a kasar Tunisia Albaji Kaid Sabisi ya bayyana cewa suna yin matukar kokarinsu domin ganin cewa sun bunkasa ayyukan babban bankin musulunci a kasar, ta yadda zai amfanar da masu son saka hannayen jari da sauran harkokin kasuwanci.
A shafin sadarwa na yanar gizo na Times of Oman an bayyana cewa, za a sanar da sakamakon gasar hardar kur’ani mai tsarki da tajwidi da aka gudanar a kasar Oman, wadda cibiyar bunkasa harkokin kur’ani ta sarki Kabus ta dauki nauyin shiryawa a birnin Maskat fadar mulkin kasar a cikin wannan wata da muke ciki rajab mai alfarma.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na da matukar muhimmanci ga matasana kasar Gambia da aka san su da mayar da hankali a kan lamurran da suka danganci addini, ya ci gaba da cewa da dama daga cikin masu bindiddigin lamurra suna ganin cewa bude wannan cibiya zai kara karfin matasa masu sha’awar karatun kur’ani, bude wata babbar cibiyar hardar kur’ani mai tsarki a birnin Crown na kasar Gambia.
814440