IQNA

An Ayyana Mahmud Tabalawi A Matsayin Magajin Sheikh Abul Ainain

16:56 - June 26, 2011
Lambar Labari: 2144725
Bangaren kasa da kasa, bayan rasuwar babban malamin addini kuma makarancin kur’ani mai tsarki na kasar Masar Sheikh Abul Ainan, an nada daya daga cikin fitattun malaman kur’ani na kasar Shekh Mahmud Al-tabalawi a matsayin magajinsa.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, bayan rasuwar babban malamin addini kuma makarancin kur’ani mai tsarki na kasar Masar Sheikh Abul Ainan, an nada daya daga cikin fitattun malaman kur’ani na kasar Shekh Mahmud Al-tabalawi a matsayin magajinsa.
Labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar yaum Sabi ta kasar Masar an bayyana cewa, an gudanar da zaman ta’aziyya na rasuwar babban malamin kur’ani kuma makaranci wato shekhul kurra na kasar Masar, wanda Allah ya yi wa rasuwa kwanaki uku da suka gabata, dukkuwa da cewa manyan malaman Azhar sun kauracewa janazarsa da kuma zaman ta’aziyar tasa.
Da dama daga cikin iyalan mamacin sun nuna matukar mamaki dangane da matakin da malaman jami’ar Azhar suka dauka na kaurace ma janazar shehin malamamin, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa harkokin kur’ani a akasar Masar, wanda ya kafa makarantun da suka samar da fitattun malaman kur’ani da makaranta da duniyar musulmi ke takama da su a halin yanzu.
An gudanar da zaman ta’aziyya na rasuwar babban malamin kur’ani kuma makaranci wato shekhul kurra na kasar Masar, wanda Allah ya yi wa rasuwa kwanaki uku da suka gabata, dukkuwa da cewa manyan malaman Azhar sun kauracewa janazarsa.
814483

captcha