IQNA

Tarayyar Turai Ta Jaddada Wajabcin Yin Adalci A kan Wadanda Aka kama A Bahrain

15:14 - July 02, 2011
Lambar Labari: 2147614
Bnagaren kasa da kasa, babbar jami’a mia kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai katrin Ashton ta bayyana cewa, kungiyar tana kira ga mahukuntan kasar Bahrain da su yi adalci kan mutanen da suka suna zanga-zangar nuna kiyayya mulkin Alkhalifa, da kuma neman gudanar da sauyi na siyasa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Al-intikad cewa, babbar jami’a mia kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai katrin Ashton ta bayyana cewa, kungiyar tana kira ga mahukuntan kasar Bahrain da su yi adalci kan mutanen da suka suna zanga-zangar nuna kiyayya mulkin Alkhalifa, da kuma neman gudanar da sauyi na siyasa da mulki a kasar, da ke fama da mulkin mulukiyya.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran AFP an bayyana cewa, mutanen kasar Bahrain sun gudanar da gagarumar zanga-zangar yin Allawadai da mahukuntan kasar da suke yin amfani da karfi wajen murkushen boren fararen hula na lumana, tare da dakarun mamaya na kasar Saudiyya, inda suka ci zarafin mutane da keta alfarmar wurare masu tsarki, kamar masallatai da wuraren gudanar da tarukan addini.
Kasar Bahrain dai na fuskar gagarumin sauyi, domin sama da kashe sab’in ciki dari na al’ummar kasar ne suka mike suna neman sauyi, sakamakon danne hakkokinsu da ake yi na ‘yan kasa, tare da mayar da su saniyar ware a cikin dukkanin harkokin mulki da siyasar kasar.
818037


captcha