IQNA

Babban Sakataren ISESCO Ya Samu lambar Yabo Ta Cibiyar Iyali Ta Duniya

11:40 - July 07, 2011
Lambar Labari: 2150387
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun muslunci Abduaziz Usman Al-tuwaijari, ya samu lambar yabo ta cibiyar kula da harkokin iyali ta duniya, wadda ke karkashin kulawar majalisar dinkin duniya, bisa namijin kokarin da cibiyar ta ce yana yi.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin yanar gizo na kungiyar ISESCO an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun muslunci Abduaziz Usman Al-tuwaijari, ya samu lambar yabo ta cibiyar kula da harkokin iyali ta duniya, wadda ke karkashin kulawar majalisar dinkin duniya, bisa namijin kokarin da cibiyar ta ce yana yi waen kula da hakkokin iyalai da kuma kulawa da su a duniya.

An gudanar mika ma Altuwaijari wannan lambar yabo ne a birnin Geneva fadar mulkin kasar Switzerland, tare da halartar wasu daga cikin manyan jami'an majaisar dinkin duniya, musamman ma ma'akata wannan cibiya, gami da wasu daga masana daga kasashen musulmi, da kuam mazauna kasashen nahiyar turai.

Babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun muslunci Abduaziz Usman Al-tuwaijari, ya samu lambar yabo ta cibiyar kula da harkokin iyali ta duniya, wadda ke karkashin kulawar majalisar dinkin duniya, bisa namijin kokarin da cibiyar ta ce yana yi a bangaren harkoki na iyalai.

821091


captcha