IQNA

A Gobe Za A Sanar Da Birnin Konakry Cibiyar Al'adun Musulunci Ta Wannan Shekara

18:08 - July 17, 2011
Lambar Labari: 2155444
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da taron shelanta birnin Konakry na kasar Guenia a matsiyin babban birni kuma cibiyar al'adun Musulunci ta shekara ta 2011 wanda cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun muslunci ta dauki nauyin shiryawa.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an ISESCO an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da taron shelanta birnin Konakry na kasar Guenia a matsiyin babban birni kuma cibiyar al'adun Musulunci ta shekara ta 2011 wanda cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun muslunci ta dauki nauyin shiryawa da za a fara daga gobe litinin idan Allah mai kowa da komai ya kai mu.
A shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa jaridar Qods arabi da ake bugawa a birnin London na kasar Birtaniya an bayyana cewa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon ta hizbullah ta yaba da furucin da ya fito daga bakin babban malamin addini na jami'ar Azhar da ke kasar Masar, da ke neman samun fahimtar juna tsakanin mabiya tafarkin sunna da kuma mabiya tafarkin ahlul baiti.

Wannan bayani da kungiyar ta fitar ya zo a lokacin da shehin malamin ya bayyana wa duniyar musulmi cewa 'yan shi'a musulmi ne kamar sauran musulmi, saboda haka babu wani dalili na mayar da su saniyar ware a cikin harkokin Musulunci, a lokacin da wasu mabiya tafarkin wahabiyanci ke ta kokarin fitar da mabiya tafarkin ahlul bait daga addini.

826346

captcha