IQNA

An Bude Hanyar Karbar Sakonnin Masu Ziyaratar Imam Hussain (AS) Ta Yanar Gizo

12:00 - July 21, 2011
Lambar Labari: 2157423
Bangaren kasa da kasa, an bude wani shafi na karbar sakonni da suka hada korafi da kuma shawarwari daga masu ziyarar habbaren Imam Husain (AS) da ke birnin karbala mai alfarma, domin sanar da bangarorin da abin ya shafa kan matsaloli ko makamanci haka da ake fuskanta.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an bude wani shafi na karbar sakonni da suka hada korafi da kuma shawarwari daga masu ziyarar habbaren Imam Husain (AS) da ke birnin karbala mai alfarma, domin sanar da bangarorin da abin ya shafa kan matsaloli ko makamanci haka da ake fuskanta alokacin gabatar da irin wannan aikin ibada na ziyara a wannan hubbare mai tsarki.

Majiyar asibiti a birnin Karbala mai alfarma a kasar Iraki sun bayyana cewa, mutane 13 aka tabbatar da sun rasa rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta'addanci da aka kai kan masu gudanar da tarukan addini a birnin.

Babban daraktan ma'aikatar kiwon lafiya reshen Karbala Dokta Ala Hammudi ya bayyana cewa, an kai hare-haren ne da bama-bamai a kan masu gudanar da ziyara a hubbaren Imam Hussain jikan manzon Allah (SAW) da ke birnin, inda ake gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) taron da ya samu halartar sama da mutane miliyan biyu da rabi daga sassa daban-daban na kasar Iraki, da kuma wasu sama da dubu 150 daga kasashen duniya daban-daban.

Dokta Hammudi ya ce mutane 13 da suka hada da mata da kanan yara sun yi shahada, gami da wasu jami'an tsaro uku, yayin da adadin wadanda suka ji raunuka ya haura mutane 100.

828659
captcha