Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kur'ani mai tsarki da aka buga a cikin harshen urdu, wanda wasu daga manyan malaman addini na jami'ar Azhar suka dauki nauyin sanya ido kan aikinsa, wanda yaznu haka yake anan cikin babban dakin gudanar da taron baje koli a birnin Tehran.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, an nuna wani kwafin kur'ani mai tsarki da aka buga a cikin harshen urdu, wanda wasu daga manyan malaman addini na jami'ar Azhar suka dauki nauyin sanya ido kan aikinsa, wanda yaznu haka yake anan cikin babban dakin gudanar da taron baje koli a birnin Tehran abban birnin jamhuriyar muslunci ta Iran.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi ya bayyana a jiya litinin cewa, ya tattauna ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Jamus inda ya bukaci kasar Jamus ta dauki mataki kan shugaban kungiyar yan ta'adda ta PJAK ta kurdawa wanda yake zaune a kasar ta Jamus.
Salihi ya ce ya bukaci Guido Westerwell ya kawo karshen ayyukan kungiyar ta kurdawan kasar Iran a kasarsa ta Jamus.
A cikin makon da ya gabata ne jami'an tsaron kasar Iran suka kai hare hare kan yayan kungiyar ta PJAK da ke ayyukan ta'addanci a yankin Kurdawa na kasar a kan iyakarta da kasar Iraqi, inda suka kashe suka kama sannan suka lalata cibiyoyin kungiyar da dama.
Shugaban kungiyar ta PJAK Rahman Haji Ahmadi ya fito a fili a makon da ya gabata a kasar Jamus inda ya bayyana cewa kungiyarsa zata ci gaba da yakar gwamnatin kasar Iran har sai yankin kurdawan ya sami 'yanci.
831307