IQNA

A Cikin watan Ramadan Mai Alfarma Ne Za A Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta UAE

15:03 - July 26, 2011
Lambar Labari: 2160395
Bangaren kas ad akasa, a cikin watan Ramadan mai alfarma ne za a gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta shekara-shekara a kasar hadaddiyar daular larabawa a birnin Fujaira, wanda shi ne na biyar da za a gudanar da ita a birnin a cikin watan mai alfarma.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa,a wani rahoton da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, a cikin watan Ramadan mai alfarma ne za a gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta shekara-shekara a kasar hadaddiyar daular larabawa a birnin Fujaira, wanda shi ne na biyar da za a gudanar da ita a birnin a cikin watan mai alfarma kamar yadda cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta kasar ta sheda.

Shugaban hukumar wucin dagin kasar Abduljalil ya ce za a kyale shugaba Muammar Gaddafi da kuma iyalansa su ci gaba da zama a cikin kasar idan suna so amma bisa wasu sharuda.
Mustafa Abduljalil ya yi wannan bayani ne a jiya Lahadi a cikin zantawa da ya yi da jaridar ta kasar Amurka. Abduljalil ya ce dole ne ya kasance hukumar wucin gadi ita ce zata zabi inda Gaddafi zai zauna kuma ita zata tura mutanen da zasu sa ido a kansa, amma da farko dole ne sai Gaddafi ya sauka daga kujerar shugabanci.
Wannan sanarwa ta Abduljalil ta zo ne a lokacin da bangarori biyu kasar masu yaki da juna da kuma wasu kasashen waje suke kara kaimi domin kawo karshen rikicin na kasar Libya.
Shugaban na hukumar wucin gadi ya kai rangadinsa na farko a birnin Zintan inda dakarun juyin juya hali suka kafa hedkwatarsu ta yanki.

831061

captcha