Kamfanin dilalncin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na lexression an byayana cewa, sama da mutane dari uku ne suka karbi addinin muslunci a kasar Algeria acikin wannan shekara ta 201 da muke ciki, bayan da suka fahimci cewa addinin musulunci shi kadai ne hanyar rayuwa maf dacewa da dan adam da kuma yadda ya kamata kasance.
Sai dai kuma wani labarin na daban yana cewa, hukumar bincike ta kasa da kasa da sarkin Bahrain Hamad bin Isa ya kafa ta fara gudanar da bincike a kan matakan da sojojin kasar suka dauka tare da taimakon sojojin kasar Saudiya domin murkushe zanga zangan kin jinin gwamnatin Khalifa.
Mutane shida wadanda ba yan kasar ba suke aiki a hukumar binciken wacce zata yi nazari akan rawar da jamian tsaro suka taka a wajen hana gangami da jerin gwanon adawa a kasar wanda kuma ake zarginsu da kashe mutane da take hakkokin bil Adama.
Hukumar zata binciki sojojin kasar ta kasar da kuma zargin da ake yi cewa sojojin kasar Saudiya na cewa sun gallaza wa yan adawa da suka kama tare da gana musu azaba.
Cibiyar kare hakkin bil Adama ta kasar wacce kungiya ce mai zaman kanta, ta ce a yanzu haka da akwai sama da mutane dubu daya da ake tsare da su a ikin kasar saboda dalilai na siyasa.
831028