IQNA

Kawo Karshen Gasar Karatu Da Hardar Kur’ani Mai Tsarki A Kasar Iraki

15:14 - July 30, 2011
Lambar Labari: 2161874
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Iraki wadda aka gudanar a birnin Bagadaza babban birni kuma fadar mulkin kasar ta Iraki, gasar da ta kebanci daliban jami’a da suka hada da mahardata da kuma makaranta daga cikinsu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyan a cewa, an kawo karshen gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Iraki wadda aka gudanar a birnin Bagadaza babban birni kuma fadar mulkin kasar ta Iraki, gasar da ta kebanci daliban jami’a da suka hada da mahardata da kuma makaranta daga cikinsu, kamar dai yadda aka saba gudanarwa.
Wani rahoton ya ce an fara rijistar sunayen masu sha’awar shiga gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Masar, wadda za a fara gudanarwa amataki na kasa, daga bisani kuma za a gudanmar da abbar gasar karatu da hardar kur’ani ta duniya baki daya a kasar, tare da halartar mahardata da makaranta daga sassa na kasashen duniya musamman na larabawa da na musulmi.
A bangare guda kuma an fara gudanar da taron baje koli na kayan fasahar masana a musulunci a kasar Birtaniyam, wanda babbar cibiyar kula da kayan tarihin muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa tun daga makon da ya gabata a babban dakin tarukanta da ke birnin London fadar mulkin kasar.
Taron yana samun halartar masana kan harkokin al’adu da tarihi daga jami’ar birnin London da kuma wasu cibiyoyi na mabiya addinin muslunci da ke cikin sassan kasar, haka nan kuma ana nuna wasu daga cikin abubuwan da aka samar na fasahar musulunci a kasar weadanda suke nuna kokarin masana musulmi masu fasaha da suke gudanar da ayyuka a wannan bagire.
833391

captcha