Bangaren kasa da kasa, ana nuna kwafin kur'ani mai tsarki a baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a karo na goma sha tara wanda shi ne irinsa na farko da ake nunawa a wannan baje koli domin raya tunanin kur'ani da koyarwarsa acikin al'umma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran cewa, ana nuna kwafin kur'ani mai tsarki a baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a karo na goma sha tara wanda shi ne irinsa na farko da ake nunawa a wannan baje koli domin raya tunanin kur'ani da koyarwarsa acikin al'ummar musulmi musamman am a wannan zaani da ake da kishi matuka dangane da koyarwar kur'ani.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wannan karon an kawo kaya da dama da suke nuna irin ci gaba da aka samu ta fuskacin kur'ani da fasahohi daban-daban a wannan bangare tsakanin matasan jamhuriyar musulunci ta Iran da suka himmatu da sha'anin kur'ani mai tsarki a kasar.
Nuna kwafin kur'ani mai tsarki a baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a karo na goma sha tara wanda shi ne irinsa na farko da ake nunawa a wannan baje koli domin raya tunanin kur'ani da koyarwarsa a cikin al'umma zai kara karfafa gwiwar matasa a wannan bagere.
Yanzu haka cibiyoyin kur'ani mai tsarki daga sassan kasar ne suke ci gaba da kawo kayansu a wurin baje kolin na kur'ani, kuma ana ganin cewa matasa da suke halartar wurin suna samun amfana daga kayan da aka kawo na kur'ani mai tsarki.
833908