Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, pira ministan kasar Norway ya halarci wanan masallaci a birnin Auslo domin taya musulmi alhini kan kisan gillar da aka yi musu a cikin makonni biyu da suka gabata, bayan da wani dan ta'adda ya kai hari kansu tare da kasha mutane sama da casa'in ba gaira ba sabar sai domin tsananin kiyayya da addinin muslunci.
Labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Lci an bayyana cewa, , za a nuna wani mushafin kur'ani mai tsarki na kasar Mauritaniya da aka kira mushafin kasa mai suna Shakit, wanda za a kammala dukkanin ayyukansa daga nan zuwa karshen wannan shekara da muke ciki ta 2011.
Bayanin ya ci gaba da cewa an rubuta wannan kur'ani mai tsarki ne da salon rubutu na kasar d ake yin amfani da shi a hukumance, kuma a cikin wannan mako da muek ciki ne za a gyara bangare kashi uku bisa hudu na mushafin da aka kammala rubutunsa a birnin Nuwakshout fadar mulkin kasar.
Yanzu haka dai ana shirin nuna wani mushafin kur'ani mai tsarki na kasar Mauritaniya da aka kira mushafin kasa mai suna Shakit, wanda za a kammala dukkanin ayyukansa daga nan zuwa karshen wannan shekara da muke ciki kamar dai yadda ma'aikar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar.
833820