Bangaren kasa da kasa, wata babbar cibiyar musulmi da ke birnin Jakarta na kasar Indonesia tana daukar nauyin buda bakin mutane dubu daya a kowace rana marayu da kuma matafiya, domin samun falalar wannan wata mai alfarma.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, wata babbar cibiyar musulmi da ke birnin Jakarta na kasar Indonesia tana daukar nauyin buda bakin mutane dubu daya a kowace rana marayu da kuma matafiya, domin samun falalar wannan wata mai alfarma kamar yadda wasu mutanen a daidaiku suke yi.
Bayanin ya ci gaba da cewa, mai kula da bangaren hulda da jama'a na wannan cibiya Paimum Abdulkarim ya bayyana an samu gagarumin ci gaba ta wannan fuska idan aka kwakwanta da shekarar da ta gabata, inda adadin abin da aka bayar ya lunka, domin kuwa a shekarar da ta wuce cibiyar ta bayar da abinci ne ga mutane dari biya a kowace domin yin buda baki.
Babbar cibiyar musulmi da ke birnin Jakarta na kasar Indonesia tana daukar nauyin buda bakin mutane dubu daya a kowace rana marayu da kuma matafiya, domin samun falalar wannan wata mai alfarma na Ramadan, kamar yadda daya daga cikin jami'an cibiyar ya sanar.
836244