Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, wannan aya mai albarka tana yin nuni zuwa ga wasu manyan laifuka biyu, da suke jawo yaduwar rashin adalci da rashin tsaro a cikin rayuwar al’umma da attalin arzikinsu, inda ake yi wa musulmi gargadi da su guje su. Na daya shi ne cin dukiyar wani ta hanyar da ba ta dace ba, na biyu bayar da rashawa ga alkalai domin mallake dukiyoyin jama’a, lamarin da ya sa aka hani musulmi da yin hakan hani mai tsanani, tare da bayyana shi a matayin babban zunubi.
Ayyukan da shari’a ta hana, ko a hankalce za a ga ba su dace da dabi’a ta dan adam ba, da ma yanayin zamantakewarsa ba, duk da cewa wasu suna bayar da cin hanci da rashawa a matsayin kyauta ko ihsani, wanda hakan ba ya taba halasta rashawa, matukar dai manufar hakan ita ce rashawar amma ta wata hanya ta daban.
Muslunci yana girma mutane da abin da suka malakka, saboda haka ba ya bayar da dama ga wani ya yi tasarrufi da dukiyar wani ba bisa ka’ida ba, kamar dai yadda ya tabbata a cikin shari'a yin azumi wajibi ne a kan dukkanin musulmi mace da na miji da suka cika sharuddansa.
840673