Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na assawsana an bayyana cewa, daga cikin masu kula da madaba'antar sarki Fahad da ke buga kur'anai a birnin Madina mai alfarma Baha'uddini Khairi saleh ya bayyana cewa an fara gudanar gwaji na shafin yanar gizo kur'ani mai sauti domin koyon karatun kur'ani mai tsarki ta wannan hanya a fadin duniya.
Wannan sura ta safka ne a Madina, ita ce kuma sura ta uku a cikin kur'ani mai tsarki, kuma an ambaci wannan sura da wannan suna ne saboda ambaton sunan Imran da aka yi a cikin aya ta 33, wannan shi ne sunan mahaifin annabi Musa (AS), kuma sunan mahaifin Maryam mahaifiyar annabi (AS) koda yake a cikin wannan sura an ambaci kissar Maryar ne da danta Isa Almasihu.
Cikin surarar da ta gabata mun yi bayani kan wadannan haruffa, cewa Allah madaukakin sarki ya bar wa kansa sanin ma'anarsu da shi da manzonsa, wanda wannan yana daya daga cikin mu'ujizoji na kur'ani mai tsarki kamar yadda bayani ya gabata a baya.
Ayar da ke bayan wannan kuwa, tana yin bayani ne kan siffofin Allah madaukakin sarki, wanda ya hada dukkanin kamala, ya tsarkaka daga duk wani aibi, ba a zatinsa ba kawai, a a hatta a cikin dukkanin siffofinsa. Allah shi kadai ne ba shi abokin tarayya, kuma dawwamamme ne har abada, sabanin mu abin halitta, a da babu mu, sannan aka samar da mu
Kuma wani lokaci zai zo da babu mu, alhali Allah haka ba ta faruwa da shi, bil hasali ma shi ne mai samarwa da rasarwa, shi kadai ne ya cancanci bautar ba yi, baya ga shi babu wani mahaluki da ya cancanci a bauta masa a matsayin ubangiji.
842211