Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalato daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, babban malamin addini na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya bayyana cewa, sakin daruruwan mutanen da ake tsare da su a gidajen kurkukun mahukunatan kasar Bahrain saboda mahangarsu ta siyasa, ba shi ne warware matsalar da ake fama da ita a kasar bat a rashin adalci da zalunci da kuma danniya, a a kan haka dole ne mahukuntan kasar su saurari abin da mutane suke fada domin karba bukatunsu.
Sau da yawa wasu kan gina akidunsu bisa dogaro da zahirin ayoyi masu kama da juna (mutashabihat) sai hakan ya kai su ga suranta Allah madaukakin sarki tamkar wani mutum ko wani abun halitta, alhali kuwa irin wadannan ayoyi na kur'ani suna bukatar tawili, kamar yadda wannan ayar ta ce babu wanda ya san tawilinsu sai Allah da kuma wadanda suka tsaga ilimi, wato annabawa da kuma wasiyyansu, da kuma wasu daga cikin salihan bayin Allah, a kan haka a irin wannan yanayi dole ne a koma gare su domin sanin ma'anar ayoyi masu kama da juna.
Wasu daga cikin ayoyin kur'ani mai tsarki suna da ma'ana sabanin zahirin ayar, a irin wannan yanayi dole ne a koma ga masana na hakika, maimakon yin gaban kai wajen fassara kur'ani bisa fahimta ta kuskure.
Ba rikici da hanayaniya ko fadace-fadace ce kawai ake nufi da fitina ba, babbar fitina ita ce a juya hakikanin akidar addini da tauhidin musulmi zuwa wani abu daban da ba haka yake a cikin addinin muslunci ba, fassara ayoyin ubangiji bisa san rai ko jahilci.
842036