Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi Allawadai da ci gaba da haka ramuka da yahudawan sahyuniya suke yi karkashin masallacin Qods mai alfarma, da kuma gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan birnin mallakin palastinawa.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani labari da ke cewa, kungiyar kasashen musulmi ta yi Allawadai da ci gaba da haka ramuka da yahudawan sahyuniya suke yi karkashin masallacin Qods mai alfarma, da kuma gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan birnin mallakin palastinawa da nufin mayar da sauran yankunan birnin mallakin yahudawan sahyuniya, kamar dai yadda duniya take gani kuma zura ido.
Wani labarin kuma da aka nakalto daga wasu kafofin sadarwar ya yi uni da cewa, palasdinawa sun gudanar da zanga zangar neman kaurace wa kayayyakin da ake sarrafa su a haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kamfanin dillancin labaran ya habarta cewa; Palasdinawa a garin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar da wata gagarumar zanga zanga a jiya alhamis domin jaddada daukan matakin kaurace wa kayayyakin da yahudawan sahayoniyya ke sarrafa su musamman kayayyakin da ake shiga da su cikin yankunan Palasdinawa daga matsugunan yahudawa 'yan kaka gida.
Zanga zangar wadda ta samu halattan dinbin jama'a da suka hada da daliban kananan makarantu da na jami'o'i sun zaga hanyoyin garin Ramallah suna rera taken Allah wadai da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da jaddada hakkin Palasdinawa na gudanar da gwagwarmaya domin kwato dukkanin hakkokinsu.
843070