IQNA

An Sanar Da Sunayen Mutanen Da Suka Nuna Kwazo A Gasar Kasar Kuwait

11:30 - August 15, 2011
Lambar Labari: 2170938
Bangaren kasa da kasa, an sanar da sunayen mutanen da suka nuna kwazo gasar harder kur'ani mai tsarki ta kasar Kuwait da aka gudanar a cikin 'yan kawanakin da suka gabata, inda yanzu haka ake ci gaba da shirin gudanar da zaman karshe domin basu kyautuka.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran KUNA na kasar Kuwait cewa, ya zuwa yanzu an sanar da sunayen mutanen da suka nuna kwazo gasar harder kur'ani mai tsarki ta kasar Kuwait da aka gudanar a cikin 'yan kawanakin da suka gabata, inda yanzu haka ake ci gaba da shirin gudanar da zaman karshe domin basu kyautuka daga hukumar shirya gasa ta karatu da harder kur'ani mai tsarki ta kasar, tare da halaratr jami'an gwamnati, da kuma wakilan cibiyoyin addini na kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa A nan an ambaci ayoyin bayyanannu (muhkamat) da kuma masu kama da juna (mutashabihat) bayyanannu a nan su ne ayoyi kamar ka ce Allah daya ne wato Allah daya ne rak, ba shi da na biyu, to irin wadannan ayoyin bayyanannu ne, amma ayoyi masu kama da juna, su ne masu bukatar a yi bayanin abin da ake nufi, domin ma'anarsu ba a fili take ba,

Kamar ayar da ta ce: Hannun Allah yana kan hannayensu, wannan aya na bukatar karin haske daga malamai wadanda sukan hakikanin tafsirin kur'ani mai tsarki, domin kuwa Allah ba jiki ba ne balantana ya kasance da hannu, ga shi kuma zahirin ayar ta ambaci cewa hannun Allah yana kan hannayensu, yayin da malaman tafsiri bisa dogaro da sahihin nassi, sun bayyana ma'anar hakan da cewa; ma'anar hannun Allah a nan ita ce karfin ikonsa da mulkinsa yana birbishin na dukkanin talikai. Haka lamarin yake a sauran ayoyi makamantan wadannan. 843088

captcha