Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran an bayyana cewa, a bangaren da ake nuna wasu kayaykin kur'ani a baje kolin da ke gudana a kasuwar baje koli ta kasa da kasa da ake gunarwa, an nuna wasu alluna da suke dauke da ayoyin kur'ani mai tsarki da aka rubuta a cikin harsuna na duniya.
A cikin shirin da ya gabata idan masu saurarenmu suna tune, mun bayyana cewa malamai sun kasu kashi biyu kan fassara ayoyin kur'ani mai tsarki, akwai wadanda suna yin amfani da ayoyin kur'ani wajen canja tunanin mutane daga sahihiyar akida ta tauhidin Allah madaukakin sarki, ta yadda za su cusa ma mutane mahangarsu da kuma yadda su suka fahimci addidi.
Amma ta hanyar yin amfani da ayoyin kur'ani mai tsarki, kamar misalin da muka bayar na ayoyi bayyanannu, da kuma masu kama da juna inda yi bayani kan cewa ayoyi muhkamat a manarsu haka take kamar yadda ya zo a zahirin aya, amma mutashabihat, ba zahirin ayar ne ma'anarsu ba, dole sai an yi tawili bisa dogaro da sahihin nassi da dalilan safkar aya da sauran hanyoyi da ake bi wajen gane tawilin aya.
Wasu daga cikin malami kuma ba su gona da iri, suna bin dukaknin hanyoyin da suka kamata wajen fassara kur'ani ba tare da saka san ransu wajen juya ma'anar ayoyin ba, to irin wadannan su ne malamai na Allah masu yin aiki da fadarsa, masu shiryar da bayinsa.
843996