Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Farmington an bayyana cewa, mabiya addinai daban-daban za su fara gudanar da wani zama a jahar Machigan ta kasar Amurka, bayan da abbabr cibiyar kula da ayyukan muslunci ta jahar ta yi kira domin gudanar da wannan zama domin tattaunawa kan muhimman abubuwa da suka hada su.
Wannan taro za a gudanar da shi ne a daidai lokacin da ake taruka na watan Ramadan mai alfarma a ko'ina cikin kasashen musulmi, da kuma sauran kasashe ma wadanda ban a musulmin ba, amma mabiya awannan addini suna gudanar da tarukansu a wannan lokaci mai albarka.
Ana fara gudanar da wannan taro ne a babban ginin cibiyar muslunci da ke birnin Kanton na jahar, daya daga cikin wadanda aka gayyata kuma mamba a wanan cibiya Cristina Rontry ta bayyana cewa, babbar manufar wannan taro ita ce yadda sauran bangarori za su samu fahimtar juna a tsakaninsu baki daya.
Rahoton ya ce mabiya addinai daban-daban za su fara gudanar da wani zama a jahar Machigan ta kasar Amurka, bayan da abbabr cibiyar kula da ayyukan muslunci ta jahar ta yi kira domin gudanar da wannan zama domin karafa zaman lafiya.
844666