IQNA

Taro Mai Taken Muhimmancin Iyali A Musulunci A Kasar Morocco

11:46 - August 18, 2011
Lambar Labari: 2173050
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken muhimmanci iyali a cikin addinin muslunci a birnin kazablanka na kasar Morocco a ranar 26 ga watan Mordad.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lematin an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken muhimmanci iyali a cikin addinin muslunci a birnin kazablanka na kasar Morocco a ranar ashirin da shida ga wannan wata.

A wani labarin kuma na daban hukumomin kasar Maroko sun bayyana cewa za'a gudanar da zaben gaggawa na 'yan majalisar dokokin kasar a tsakiyar watan nuwambar wannan shekara idan Allah ya kai mu, a matsayin wani mataki na kauce wa kasar fadawa a irin halin da kasashe da dama na larabawa suka fada.
Firaministan kasar ta Maroko Abbas Al-Fassi ne ya tabbatar da hakan.

Yana mai cewa an zabi wannan lokaci domin gudanar da zaben ne bayan wata ganawar da aka yi tsakaninsa da kuma wakilan jam'iyyun siyasar kasar duk da cewa wasu daga cikin jam'iyyun sun bukaci da a gudanar da zaben a cikin watan Oktoba mai zuwa.

A jawabin da ya gabatar wa al'ummar kasar a ranar 30 ga watan yulin da ya gabata, Sarki Muhammad na 6 wanda a lokacin yake fusknatar matsin lamba daga al'ummar kasar, ya sanar da yin sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar, sauye-sauyen da suka hada har da rage karfin ikon Sarkin da kuma bai wa firaminista karin iko.

845218
captcha