IQNA

Masu Fasaha A Cikin Msulunci Ya Kamata Su Ma Masu Isar Da Sakonsa

16:10 - August 22, 2011
Lambar Labari: 2175001
Bangaren kasa da kasa, ayyukan fasaha na addinin muslunci suna daga cikin hanyoyin da suka fi dacewa kuma suke yin tasiri cikin sauki wajen isar da sakon muslunci ga sauran al’ummomin duniya a wannan zamani da muke rayuwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya gudanar da wata tattaunawa tare da wani malamin jami’a a kasar Tunisia da ke halartar taron baje kolin littafan kur’ani Munsef Hamidi, wanda ya bayyana cewa ayyukan fasaha na addinin muslunci suna daga cikin hanyoyin da suka fi dacewa kuma suke yin tasiri cikin sauki wajen isar da sakon muslunci ga sauran al’ummomin duniya a wannan zamani da muke rayuwa bisa la’akari da gagarumin ci gaban da ke samu ta wannan bangare.
Wasu daga cikin ahlul kitab a lokacin ma'aki (SAW) duk da masaniyar da suke da ita ta zuwan kur'ani mai tsarki daga Allah madaukin sarkin bayan littafan Attauara da Injinla, amma ba a shirye suke ba su yi imani da manzon karshe, kuma su karbi kur'ani mai tsarki a matsayin littafin da ya zo daga Allah madaukakin sarki.

Wannan aya ta ba su amsa da cewa, a tsawon tarihi Allah yan aaiko annabawa domin shiryar da mutane, wasu daga cikinsu ana bas u sha'ri'a da littafi, dukaknin wadannan annabawa sun gasgata junasu, saboda dukakninsu daga Allah ubagiji daya suke, kuma sakonsa ne suke isarwa ga 'yan adam. A kan haka babu wani abun mamaki, domin kuwa ubangijin da ya safkar da Attauara ga annabi Musa (AS) ya safkar da Injila ga annabi Isa (AS), shi ne ya safkar da kur'ani ga manzon Muhammad (SAW)

Saboda haka wannan aya ta gaya musu cewa idan da gasket suna neman gaskiya ne, to wajibi ne su yi iani da annabi Muhammad da sakon da ya zo da shi daga Allah.
847368


captcha