IQNA

Shirin Gasar Kur’ani Mai Tsarki Na Yara Maza Da Mata A Kasar Algeria

16:09 - August 22, 2011
Lambar Labari: 2175002
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da shirin gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki na kananan yara a kasar Algeria wanda aka yi wa take da Tajul kur’an, da gidan talabijin din kasar ya watsa kai tsaye.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar al-khabar an bayyana cewa, an gudanar da shirin gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki na kananan yara a kasar Algeria wanda aka yi wa take da Tajul kur’an, da gidan talabijin din kasar ya watsa kai tsaye ga masu kallo.
Daga daga sayun zalunci shi ne rafkana daga ubangiji, alhali babu wani lokaci da mutum ba ya karkashin ikon ubangiji, kuma yana gani da sauren dukkanin ayyukan mutum, ba ma ta mutum ba wanda adadinsa ko alama bai kai halittun Allah da ke cikin sammai da kassai ba, wadanda su ma Allah yana tare da su, yana da masaniya kan dukkanin abin da suke yi, bil hasali ma shi ne ke ikon tafiyar da su baki daya.
Babu abin da ke buya ga Allah, a cikin sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, hatta ma jariri da ke cikin mahaifa samuwarsa tana hannun Allah, shi ne yake tsara halittar jinjiri a cikin mahaifa har kai lokacin da zai gama girma a haife shi, ya raya shi ya kare shi, lallai Allah shi ne mai hikima.
847396

captcha